✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kotun Koli ta halasta wa Ahmed Lawan takarar Sanatan Yobe ta Arewa

Bashir Machina ya gaza gabatar da hujjar baka ta zargin aikata magudi a zaben fitar da gwanin.

Kotun Kolin ta tabbatar da Sanata Ahmad Lawan a matsayin halastaccen dan takarar kujerar Sanatan Yobe ta Arewa.

Da yake yanke hukunci, Alkalin Kotun Mai Shari’a Centus Nweze ya ce Bashir Machina ya gaza gabatar wa Babbar Kotun Tarayya da ke Damaturu hujjar – baka ta zargin aikata magudi a zaben fitar da gwanin – da ya sa ake gayyatar bangaren Ahmad Lawan zuwa kotun.

Jam’iyyar APC ce dai ta kalubalanci Bashir Machina a matsayin dan takararta na kujerar Sanatan Yobe ta Arewa, tana mai cewa Ahmad Lawan ta sani a matsayin halastaccen dan takara.

A zaman sauraron karar da ya gabata, lauyan APC, Sepiribo Peters ya ce zaben fitar da gwanin da ya bai wa Machina nasara, ya saba wa Dokar Zabe ta 2022.

Peters ya ce ba jam’iyyar ce ta nada Danjuma Manga a matsayin jami’in da ya jagoranci zaben fitar da gwanin ba.

Ya shaida wa kotun cewa jam’iyyar APC ta soke zaben fitar da gwanin sakamakon matsalolin da aka samu a lokacin gudanar da zaben.

Haka kuma a cewarsa, kwamitin gudanarwar jam’iyyar ya sake shirya wani zaben fitar da gwanin ranar 9 ga watan Yuni, inda kuma Ahmad Lawan ya yi nasara.

To sai dai lauyan Bashir Machina, Sarafa Yusuf ya ce Shugaban Majalisar Dattawan bai kalubalanci hukuncin da kotunan baya suka yi ba.

Ya kara da cewa mutumin da ya jagorancin zaben da ya bai wa Machina nasara mamba ne a Kwamitin Gudanarwar jam’iyyar, wanda kuma aka nada domin ya jagoranci zaben fitar da gwanin.

Gabanin wannan, Babbar Kotun Tarayya da ke zamanta a Damaturu, ta umarci Hukumar Zabe ta Kasa INEC ta dauki Machina a matsayin dan takarar kujerar Sanatan Yobe ta Arewa.

Yayin da take yanke hukuncin, Mai Shari’a Fadimatu Aminu, ta kuma umarci jam’iyyar APC da ta mika sunan Machina a matsayin hastaccen dan takarar da ya lashe zaben fitar da gwani da aka gudanar a ranar 28 ga watan Maris na 2022.