Kotun Koli ta Najeriya ta haramta wa gwamnoni rikewa da kuma gudanar da kudaden kananan hukumomin jihohinsu.
Mai Shari’a Emmanuel Agim na Kotun Koli ya kuma ba da umarnin tura wa kananan hukumomi kudadensu kai-tsaye daga asusun Gwamnatin Tarayya.
Ya bayyana cewa ce rike kudaden kananan hukumomi da aka tura daga asusun Tarayya da gwamnatocin jihohi suke yi ya saba wa kundin tsarin mulkin Najeriya.
Don hakam yake sanar da hukuncin a ranar Alhamis, Mai Shari’a Emmanuel Agim, ya ba da umarnin damka wa kananan hukumomi 774 da ke fadin kasar kudadensu su ci gaba da gudanarwa.
- Kawu Sumaila ya miƙa ƙudirin ƙirƙiro sabuwar jiha daga Kano
- Yanzu burodi da wake sun gagare mu — Leburori
- Tubabbun ’Yan Boko Haram 560 Sun Fara Koyon Sana’o’i A Borno
Alkalin ya kuma kori buƙatar da gwamnatocin jihohi suka shigar na kalubantar neman hana su tasarrufi da kudaden kananan hukumomin.
Ya bayyana cewa a tsawon lokacin da jihohi suka ki ba wa kananan hukumomi ’yancin tafiyar da kudaden, gwamnatocin jihohin ne ke yin gaban kansu da kudaden.
Kananan hukumomi 774 da ke kasar sun gamu da cikas sakamakon yadda gwamnonin ke gudanar da kudadensu.
Duk da haka, ana zargin gwamnonin da karkatar da kudaden da aka ware don gudanar da kananan hukumomi.
Neman ’yancin kudaden kananan hukumomi
A ’yan watannin da suka gabata, kiraye-kirayen neman ’yancin cin gashin kan kananan hukumomi wajen gudanar da kudadensu ya karu a Najeriya, wanda shugaba Bola Tinubu ya goyi bayan kiran.
A watan Mayu ne Gwamnatin Tarayya ta hannun Babban Lauyan Gwamnati kuma Ministan Shri’a, Lateef Fagbemi, ta maka gwamnonin jihohi 36 a kotu bisa zargin karkatar da kudaden kananan hukumomi.
A halin yanzu, Gwamnatin Tarayya tana samun kashi 52.68%, jihohi na samun kashi 26.72%, sannan kananan hukumomi na samun kashi 20.60% na kudaden shiga na ƙasar a kowane wata daga Kwamitin Allocation na Tarayya (FAAC).
Amma kuma, ana biyan kudaden kananan hukumomin ne a cikin asusun hadin gwiwa da gwamnatocin jihohi da kananan hukumomi ke gudanarwa.
A karar da gwamantin ta shigar, ta nemi a ba da umarnin hana gwamnonin wofinta da zababbun shugabancin kananan hukumomi ba bisa ka’ida ba.
Gwamnonin jihohi 36, wadanda ake tuhuma a karar, sun ki amincewa da hukumin ministan na shigar da karar.
Amma a hukuncin da ya yanke, Mai shari’a Agim ya ce ministan na da ’yancin shigar da kara da kuma kare kundin tsarin mulki.
Don haka Kotun Kolin ta bayar da umarnin cewa daga yanzu a rika biyan kananan hukumomi kudadensu daga asusun tarayya kai tsaye, ba ta hannun asusun gwamnatin jiha ba.
Mai shari’a Agim ya yi nuni da cewa rike kudaden kananan hukumomi da gwamnonin jihohi suke yi ya wargaza ayyukan kananan hukumomin.
Mai shari’a Agim ya bayar da umarnin a bi hukuncin nan take, inda ya ce babu wata gwamnatin jiha da za a mika wa kudaden kananan hukumomi.