✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kotun Ƙoli ta soke hukuncin Kotun Daukaka Kara kan Zaben Filato

Korafin da jam’iyyar APC ta shigar na kalubalantar zaben gwamna Muftwang ba su da tushe balle makama.

Kotun Ƙoli ta soke da hukuncin da Kotun Daukaka Kara ta yanke na tsige Gwamnan Jihar Filato Caleb Muftwang na jam’iyyar PDP.

A wannan Juma’ar ce wani kwamitin alkalai mai mambobi biyar ya bayyana cewa daukaka karar da Gwamna Muftwang ya yi na bisa turba ta cancanta.

Hukuncin da Mai shari’a Emmanuel Agim ya karanta, ya ce koke-koken da Nentawe Yilwatda Goswe da jam’iyyar APC suka shigar na kalubalantar zaben gwamna Muftwang ba su da tushe balle makama.

Kwamitin ya ce batun tsayar da dan takara hurumin cikin gida ne da ya shafi jam’iyya, inda ya kara da cewa jam’iyyar PDP ta bi umarnin da babbar kotu ta bayar na gudanar da zaben fidda gwani.

Aminiya ta ruwaito cewa, a wannan Juma’ar ce kuma Kotun Ƙolin ta tabbatar da nasarar gwamnonin jihohin Legas, Bauchi, Kano da Zamfara.