Babbar Kotun Jihar Kano da ke zamanta a Miller karkashin jagorancin Mai shari’a Halima Sulaiman ta yanke wa wata matar aure hukuncin daurin rai-da -rai sakamakon kashe dan kishiyarta.
Mai gabatar da kara Barista Rabi’a Sa’ad ta shaida wa kotun cewa, a 2021 ce Rukayya ta jefa dan kishiyarta a rijiya lamarin da ya yi sanadiyyar rasuwarsa.
- Gobara ta halaka wani yaro dan shekara 4 a Kano
- Yadda wasan Najeriya da Afirka ta Kudu ya yi ajalin mutum 5 saboda faɗuwar gaba
A cewarta, laifin da ake zargin matar da shi ya saba da sashe na 221 na Kundin Pinal Kod.
A yayin gudanar da shari’ar mai gabatar da kara ta gabatar wa kotun shaidu hudu.
Lauyan wadda ake zargi, Barista Rilwan Muhammad ya roki kotun da ta yi wa wacce aka kama da laifin sassauci kasancewar tana da kananan yara da take kulawa da su.
A wani labarin kuma, wata Babbar Kotun Jihar Kano karkashin jagorancin Mai shari’a Zuwaira Yusuf ta gurfanar da wata matar aure mai suna Shamsiyya Ashiru Gabasawa bisa tuhumar ta da laifin kashe dan kishiyarta.
Mai gabatar da kara, Barista Lamido Sorondinki ya shaida wa kotun cewa, wacce ake zargin ta shayar da dan kishiyarta wanda yake jariri ne mai suna Naziru Ashiru wata guba lamarin da ya yi sanadiyyar rasuwarsa.
A cewar Sorondinki laifin da ake tuhumar matar da shi laifi ne da ya saba wa sashe na 221 na Kundin Pinal Kod.
Wacce ake tuhumar ta musanta zargin aikata laifin da ake zargin ta da shi.
Lauyan wadda ake zargi, Barista Samir Rabiu ya nemi kotun da ta bayar da belin wacce yake karewa, inda kotun ta yi fatali da rokon nasa.