Wata Babbar Kotu a Jihar Ondo ta yanke wa wasu mutum uku hukuncin kisa ta hanyar rataya bayan da ta kama su da aikata laifin kisa.
Wadanda lamarin ya shafa na daga cikin mutum hudun da ake zargi da kashe wata mata ‘yar shekara 58, diya ga jagorar kabilar Yarabawa, Mrs Funke Olakunri.
- Yadda bolar bayan gidan sarki take jefa Kanawa a cikin kunci
- Hajji 2022: Sahun farko na alhazzan Najeriya sun isa Saudiyya
Tun a 2019 ne Babban Lauyan Jihar Ondo ya gurfanar da Mohammed Usman da Osagie Lawal da kuma Adamu Adamu a kotu a kan batun kisan Olakunrin.
Laifin kisa da garkuwa na daga cikin laifukan da aka tuhume su da aikatawa a kotun.
Sa’ilin da yake yanke hukunci, Alkalin Kotun, Mai Shari’a William Olamide, ya wanke mutun na hudu mai suna Abubakar daga laifin kisan, sai dai an same shi da laifin bayar da taimako wajen aikata laifin.
Alkalin ya ce mai tuhuma ya gabatar wa kotun gamsassun bayanai wanda daga bisani kotun ta yanke hukunci bayan ta saurari lauyoyin duka bangarorin.
Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya NAN ya ruwaito Mista Charles Titiloye shi ne ke zaman lauyan mai gabatar da kara, yayin da Mista Obafemi Bawa ya kasance lauya mai kare wadanda ake tuhuma.