✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kotu ta yanke wa miji da mata hukuncin rataya a Jigawa

Wata Babbar Kotu da ke zamanta a Jihar Jigawa ta yanke wa wani miji da mata, da wasu ’yan uwanta biyu — namiji da mace— …

Wata Babbar Kotu da ke zamanta a Jihar Jigawa ta yanke wa wani miji da mata, da wasu ’yan uwanta biyu — namiji da mace—  hukuncin kisa ta hanyar rataya.

Alƙalin Kotun, Mai Shari’a Birnin Kudu ne ya yanke hukuncin bayan ya samu waɗanda ake tuhumar da laifin kashe wata mata mai suna Salamatu Musa mai shekara 30 bayan sun yi zarginta da maita.

Kotun ta yanke hukuncin a wannan Larabar, 4 ga watan Disamba a shari’ar da aka shafe tsawon lokaci tun bayan kama waɗanda lamarin ya shafa a shekarar 2019.

Bayanai sun ce waɗanda aka yanke wa hukuncin waɗanda mazaunan garin Kwan-Dole na Ƙaramar Hukumar Malam Madori sun lakaɗa wa Salamatu duka da itace bayan sun yi zargin ta lashe musu ɗansu.

Hukuncin wanda Mai Shari’a Birnin Kudu ya ce yana da madogara a sassa na 97 da 221 (7) na Kundin Dokokin Laifuka, ya ce waɗanda abun ya shafa suna da kwanaki 90 su ɗaukaka ƙara.