✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kotu ta yanke wa mawaki R-Kelly hukuncin shekara 30 a kurkuku

Kotun ta sake shi da laifin cin zarafin mata

Kotu ta yanke wa fitaccen mawakin nan na kasar Amurka, Robert Kelly wanda aka fi sani da R-Kelly hukuncin daurin shekara 30 a gidan gyaran hali.

An yanke wa mawakin wannan hukuncin ne bayan samunsa da laifin cin zarafin mata kanana da safararsu.

A watan Satumba ne wani lauya a New York ya tabbatar da zargin da ake yi wa mawakin da safarar kananan mata da cin zarafinsu na sama da shekara 30 da ya yi a masana’antar wakar Amurka.

Da take bayar da shaida a gaban kotu, wata mata da ta ce ya taba cin zarafinta mai suna Lizette Martinez wadda yanzu take da shekara 45 a duniya ta ce lokacin da suka hadu, burinta shi ne ta zama mawakiya, wanda haduwarsa ya sa ta fara murnar ta kusa cika burinta.

Ta ce bayan ya amince zai taimaka, amma bayan wata biyu da haduwarsu sai labarin ya canja, inda a cewartsa ya fara nemanta.

“Na shiga mamaki matuka, har na rika yin kuka.”

A cewarta, duk lokacin da ta tuna irin cin zarafinta da ya yi, takan shiga damuwa.

“Ka tarwatsa rayuwar mutane da dama,” inji Uwargida Martinez a gaban kotu a yayinda take nuni zuwa ga R. Kelly.

Ita ma wata mai suna Jane Doe No 2 ta ce ta so ne a ce mawakin zai kare rayuwarsa a gidan yari saboda irin cin zarafinta da ya yi.

A cewarta, da farko ta yi farin ciki ne ganin fitaccen mutum ya nuna mata kauna, amma daga baya ya rika cin zarafinta da karfin tuwo.

Sai dai zuwa yanzu ya kai kusa da shekara uku a daure.

A yanzu haka akwai sauran tuhume-tuhume guda uku da yake fuskanta da suma zai jira hukuncinsu.