Wata Kotun Laifuka na Musamman da ke Ikeja a Jihar Legas, ta yanke wa wani malamin makaranta hukuncin daurin shekara bakwai a gidan kaso bisa laifin yi wa wata dalibarsa ’yar shekara 16 fyade a cikin makaranta.
Da yake yanke hukuncin, Alkalin kotun Mai Shari’a Oluwatoyin Taiwo ya ce, mai tuhumar ya kasa ba da shaida a kan wanda ake kara, haka ma wadda lamarin ya shafa ba ta bayyana a kotu don ba da shaida ba.
- HOTUNA: Ziyarar Sarki Sunusi II a taron Majalisar Dinkin Duniya
- Kotu ta yanke wa Evans hukuncin shekaru 52 a gidan wakafi
“Sai dai, ikirarin da mai kare kansa ya yi a gaban kotun ba tare da wata tilastawa ba, ya nuna lallai ya aikata laifin.
“Mai kare kansa ya yi ikirarin ya taba nonon yarinyar sau biyu, kuma ya yi yunkurin kwanciya da ita amma hakan bai auku ba sa saboda budurcinta.
“Don haka kotu ta kama mai kare kansa da laifin yi wa yarinya karama fyade,” in ji Alkalin.
Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN), ya rawaito cewa, mai laifin ya roki kotu kan ta yi masa sassaucin hukuncin da ta yanke masa.
Ka na ya yi nadamar abin da ya aikata tare da alkawarin hakan ba zai sake aukuwa ba.
Sai dai Mai Shari’ar ya nuna masa cewa, “Kai fa malami ne sannan ka je kana taba nonon dalibarka. Da a ce wadda abin ya shafa ta zo kotu ta ba da shaida, da ka karasa rayuwarka a kurkuku.”
Da farko, hukuncin daurin shekara biyar Alkalin ya yanke wa mai laifin, amma daga bisani ta kara masa shekara biyu suka zama bakwai ba tare da wani zabi na biyan tara ba.
Wannan dai ya biyo bayan cewa an taba yanke wa wanda ake karar hukuncin daurin shekara uku a kurkuku a baya.