Wata kotu a kasar Yemen ta yanke wa Shugaban Kasar Amurka, Donald Trump hukuncin kisa bayan samun hannunsa a harin da aka kai kasuwar Dhahyan da ke Arewacin Kasar Yemen a bara.
Kotun ta zartar da hukuncin ne kan Shugaban Amurka da wasu mutum 9 ciki har da Sarki Salman Bin Abdulaziz Al-Saud na Saudiyya da kuma Yarima Muhammad Bin Salman Abdulaziz Al-Saud.
Kamfanin dillancin labarai na Saba mallakar ‘yan Houthi, ya ce hukuncin ya biyo bayan wani hari na sama da aka kai a shekarar 2019, bisa jagorancin rundunar sojin Saudiyya kan wata motar bas da ya kashe mutum 51 ciki har da yara 40 a Yemen.
Baya ga haka kotun ta nemi wadanda aka zartar da hukuncin a kansu da su biya diyyar Dala Biliyan 10 ga ‘yan uwan mutanen da rayukansu suka salwanta sakamakon harin da aka kai a bara.
Sauran wadanda hukuncin kisan ya shafa sun hada da Kwamandan Sojin Saman Saudiyya, Turki bin Bandar bin Abdulaziz, da Shugaban kasar Yemen Abedrabbo Mansour Hadi.
Haka kuma hukuncin ya shafi Mataimakin Shugaban kasar Yemen Ali Mohsen Saleh Al-Ahmar, Farai minista Ahmed bin Dagher, Ministan Tsaro Muhammad Al-Maqdishi, da tsohon Sakataren Tsaro na Amurka James Norman Mattis.
Tun a shekarar 2014 ne dai Gwamnatin Kasar Yemen ta ke yaki da ‘yan tawayen Houthi wanda suke samun goyon bayan Iran da a yanzu sun mamaye kusan dukkanin yankin Arewacin kasar da kuma birnin Sana’a.