✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kotu ta yanke wa barawon kaji hukuncin bulala 8 a Kaduna

An sami mutumin da satar kaji masu rai guda 10

Wata kotun majistare da ke Jihar Kaduna a ranar Laraba ta umarci a tsula wa wani mutum bulala 8 saboda samun shi da laifin satar kaji masu rai guda 10.

Alkalin kotun, Mai Shari’a Ibrahim Emmanuel, ne ya yanke masa hukuncin ranar Laraba, inda ya gargade shi da ya zama mutumin kirki a nan gaba.

Wanda aka yanke wa hukuncin dai ya amsa laifin da aka zarge shi da aikatawa na sata da kuma ketara iyaka, inda ya bukaci a yi masa sassauci tare da alkawarin gyara halinsa a nan gaba.

Tun da farko dai dan sanda mai shigar da kara, Chidi Leo, ya shaida wa kotun cewa wani mutum, mai suna Sani Rabi’u ne ya kai karar ga ofishin ’yan sanda na Gabasawa ranar 13 ga watan Mayu.

Ya ce mutumin tare da wasu su biyu, wadanda yanzu haka suka riga suka cika wandonsu da iska, sun saci kajin ne guda 10 masu rai a wani gidan gona da ke unguwar Kawo, a Kaduna.

Dan sandan ya ce an kama mutumin ne lokacin da yake kokarin guduwa da kajin, wadanda ya kunshe a cikin wani buhu.

A cewarsa, laifin ya saba da tanade-tanaden sassa na 308 da 233 da kuma 217 na kundin Penal Code na Jihar Kaduna na shekara ta 2017.