✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Kotu ta yanke mata daurin rai-da-rai kan mutuwar mijinta

Ita da saurayinta sun kashe mijinta don su mallake inshora ta miliyan 800

Wata kotun yankin Incheon a Koriya ta Kudu ta yanke wa wata mata hukuncin daurin rai-da-rai saboda kama da hannu a mutuwar mijinta.

Bayanan da kotun ta samu sun nuna matar da saurayinta ne suka yi sanadiyar mutuwar mijin nata a wani rafi a 2019, don su samu damar mallake inshora ta miliyan 800 a kudin kasar ($563,976) da yake da ita.

An ce Lee Eun-hae tare da saurayinta, Cho Hyun-soo, sun ja marigayin zuwa rafi a yankin Gapyeong, alhali bai iya ninkaya ba, wanda hakan ya yi sanadiyar ruwa ya tafi da shi.

Bincike ya nuna kafin jan marigayin zuwa rafi, masu laifin sun taba yunkurin hallaka shi amma ba su yi nasara ba.

Yayin da aka yanke wa matar daurin rai-da-rai, shi kuwa saurayin zaman kurkuku na shekara 30 kotu ta yanke masa.