✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Kotu ta yanke hukuncin kisa ga Faston da ya kashe yaro ya binne gawar a coci

Ya aikata laifin ne a shekarar 2017

Wata kotun Majistare da ke Ikeja a jihar Legas ta yanke wa wani Fasto mai suna Erinmole Adetokunbo da abokinsa Adedoyin Oyekan hukuncin kisa saboda kashe wani yaro don yin tsafi da shi.

Alkalin kotun, Oluwatoyin Taiwo, ta yanke hukuncin kisa ga wadanda ake zargin ranar Talata bayan sun amsa laifin.

Dan sanda mai gabatar da kara tun farko ya shaida wa kotun cewa wadanda ake zargin sun aikata laifin ne ranar bakwai ga watan Yunin 2017 a unguwar Ikorodu da ke jihar ta Legas.

Ya kuma ce Faston da abokinsa sun yanke kan yaron ne inda suka binne shi a kan mumbarin coci, suka kuma wulla sauran gangar jikin a kogi.

Bayan sauraren bangarorin biyu, alkalin kotun ta ce wadanda ake zargin sun aikata laifin ne da gangan, kuma laifin ya saba wa sashe na 222 na kundin manyan laifukan jihar, tare da zartar musu da hukuncin kisa.

An dai tsare Faston da abokin nasa ne tun a shekarar 2017, bisa zarginsu da laifin hadin baki da kisan kai.

Da fari dai sun musanta zargin, har sai da bangaren masu gabatar da kara ya gabatar da gamsassun hujjoji da shaidu, sannan suka amsa laifin nasu.

%d bloggers like this: