✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Majalisar Edo ta tanadi hukuncin kisa kan masu garkuwa da mutane

A baya dai hukuncin ɗaurin rai da rai aka tanada ga duk wanda aka tabbatar wa laifin garkuwa da mutane a Edo.

A yunƙurin daƙile ta’adar garkuwa da mutane, Majalisar Dokokin Jihar Edo, ta amince da dokar zartar da hukuncin kisa kan duk wanda aka kama da laifin.

Majalisar ta amince da ƙudirin ne wanda ta yi wa bita daki-daki yayin zaman da ta gudanar a ranar Talata.

Shugaban masu rinjaye na majalisar, Charity Aiguobarueghian ne ya jagoranci gabatar da ƙudirin wanda shugaban marasa rinjaye, Henry Okaka ya goyi baya.

A baya dai Majalisar Dokokin Edo ta ayyana hukuncin ɗaurin rai da rai ga duk wanda aka tabbatar wa laifin garkuwa da mutane tare da ƙwace duk wani abu da mallaka a dalilin aikata ta’adar ta garkuwa da neman kuɗin fansa.

Sai dai a yanzu majalisar dokoki ta sahale a tsananta matakin da za a riƙa ɗauka zuwa hukuncin kisa haɗi da ƙwace duk abin da aka mallaka ta hanyar aikata laifin.

Tuni dai Kakakin Majalisar, Blessing Agbebaku ya umarci Magatakardan majalisar da ya miƙa wa Gwamna Godwin Obasake ƙudirin domin amincewa.

Kazalika, majalisar ta amince da ƙudirin yi wa dokokin hukumomin samar da wutar lantarkin jihar gyaran fuska.