Segun Olowookere, wanda ya shafe sama da shekara 10 yana jiran a zartar masa da hukuncin kisa kan laifin satar kaji, zai samu ’yanci bayan da Gwamnan Jihar Osun, Ademola Adeleke, ya yi alƙawarin yi masa afuwa.
A shekarar 2010, Olowookere, wanda yake ɗan shekara 17 a lokacin, an kama shi tare da wani mutum mai suna Morakinyo Sunday, kan zargin haɗa baki wajen kai hari gidan wani ɗan sanda.
- An ƙulla sabuwar alaƙa tsakanin Sanata Lamido da PDP a Sakkwato
- Kasafin 2024 zai kai watan Yunin 2025 – Akpabio
Sun je gidan gonar ɗan sandan ɗauke da bindiga da adda, inda suka yi masa sata.
A 2014, mai shari’a Jide Falola na Babbar Kotun Jihar Osun, ya yanke wa Olowookere da Morakinyo hukuncin kisa ta hanyar rataya bayan samun su da laifi.
Wannan hukunci ya jawo cece-kuce a Najeriya, inda mutane da dama suka ce ya yi tsauri.
Daga nan aka kai su gidan yari na Kirikiri da ke Jihar Legas, inda aka tsare su a ɓangaren masu jiran hukuncin kisa.
Sai dai a ranar Talata, gwamna Adeleke ya bayar da umarni a yi wa Olowookere afuwa.
Gwamnan ya bayyana hakan a shafinsa na X: “Na bayar da umarni ga Kwamishinan Shari’a da ya fara aikin yin afuwa ga wannan matashin. Osun jiha ce ta adalci da daidaito. Dole ne mu tabbatar da kare rayukan al’umma da yin adalci.”
Amma har yanzu ba a san makomar Morakinyo Sunday ba, wanda tare aka yanke masa hukuncin kisa tare da Olowookere, domin ba a ambaci sunansa ba a sanarwar gwamnan.
Iyayen Olowookere da ƙungiyoyin kare haƙƙin bil’adama sun jima suna fafutukar ganin an sako shi.
Ana sa ran za a sake shi a farkon shekarar 2025.
Rabon da a aiwatar da hukuncin kisa a Najeriya tun a shekarar 2012, amma akwai sama da mutum 3,400 da ke jiran a zartar musu da hukuncin kisa.