A ranar Juma’a ne aka yanke wa direban da ya kashe mutane 35 a wani harin mota da ya kai a birnin Zhuhai da ke kudancin ƙasar China a watan da ya gabata, kamar yadda kafafen yaɗa labaran ƙasar suka rawaito.
A ranar 11 ga watan Nuwamba, Fan Weiqiu mai shekara 62 ya tuƙa ƙaramar motarsa ƙirar SUV da gangan ya afka cikin gungun mutane da suke atisaye a wajen wani rukunin wasanni.
- Lalacewar jirgin ƙasa ya sa fasinjoji sun maƙale a Delta
- Rufe ‘boda’ ya kawo yunwa da rashin aiki a Arewa —CNG
Wannan lamari da aka bayyana a matsayin hari mafi muni da aka kai a ƙasar China tun shekara ta 2014.
An tsare shi a wurin da abin ya faru, an same shi da raunukan wuƙa daga bisani kuma ya faɗi ya sume, a cewar ‘yan sanda.
An yi shari’ar Fan a bainar jama’a a ranar Juma’a, kuma kotu ta yanke hukuncin a wannan rana, cewar tashar talabijin ta CCTV ta jihar.
Kotun ta bayyana dalilin da ake tuhumar wanda ake tuhuma a matsayin “mugu,” kuma tana cewa laifin ya kasance cikin mummunan yanayi da rashin tausayi, kuma ya haifar da mummunan sakamakon, tare da cutar da al’umma.
Fan ya amsa laifinsa yayin shari’ar, wanda ya samu halartar wasu iyalan waɗanda lamarin ya shafa, da jami’ai mahukunta da sauran jama’a, kamar yadda rahotanni suka bayyana.
Kotun ta yanke hukuncin cewa Fan ya kai harin ne don “warware fushinsa” kan “Rabuwar aurensa da aka yi, da takaicin da ke damunsa da rashin gamsuwa da rabon dukiya bayan rabuwar aurensa.”