✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kotu ta yanke wa mutum 5 hukuncin rataya a Kano

Sun bi dattijuwa ’yar shekara 67 gona ɗauke da makamai suka yi mata kisan gilla

Babbar Kotun Jihar Kano ta yanke wa wasu mutum biyar hukuncin kisa ta hanyar rataya saboda laifin lashe wata dattijuwa mai shekara 67, kan zargin ta da maita.

Kotun ya yanke musu hukuncin kisa ne a ranar Litinin bayan samun su da laifin kiran dattijuwar mai suna Ɗahare Abubakar, mayya sannan suka daɓa mata wuka har lahira.

Mai Shari’a Usman Maido, ya bayyana cewa masu gabatar da ka to sun gabatar da gamsassun hujjoji da suka tabbatar da laifin wadanda aka gurfanar.

Waɗanda kana yanke wa hukuncin kisan su ne Da’luta Ibrahim, Abdulaziz Yahaya, Faisal Yahaya, Ibrahim Abdu da Ayuba Abdulrahman.

Tun da farko, mai gabatar da kara, Lamiɗo Abba-Soronɗinki, ya shaida wa koyon cewa da misalin karfe 8.30 na safiyar ranar 23 ga watan Nuwambar shekarar 2023 ne waɗanda ake tuhumar suka hada baki wajen yin aika-aikan.

Ya ce bayan waɗanda ake tuhumar sun zargi Marigayiya Ɗahare da maita ne suka bi ta gona ɗauke da makamai, suka yi mata kisan gilla,

Ya ce an garzaya da ita zuwa Babban Asibitin Wudil inda likitoci suka tabbatar cewa ran dattijuwar ya yi halinsa.

Lamarin ya faru ne a ƙauyen Daɗin Kowa da ke Ƙaramar Hukumar Wudil.