✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Kotu ta umarci mai fyade ya wanke kayan duk matan garinsu

Matashin zai yi wata shida yana wanke kayan matan garin yana kuma gogewa.

Kotu ta yanke wa wani matashi hukuncin wanke tufafin duk matan garinsu na tsawon wata shida, saboda ya yi yunkurin yi wa wata mata fyade.

Alkalin kotun da ke zamanta a Jihar Bihar na kasar Indiya, ya ce matashin mai suna Lalan Kumar zai kuma rika goge kayan matan su kusan 2,000 a kauyen na Majhor da ke Jihar ta Bihar.

Kotun ta kuma bayyana cewa matashin mai shekara 20 zai rika amfani da kudinsa wajen sayen sabulu da duk abin da ake bukata na wankewa da kuma goge kayan matan garin nasu.

Alkalin kotun ya bayar da umarnin ne a lokacin da bayar da belin Kumar – mai sana’ar wanki da guga – wanda aka gurfanar a gaban kotun.

Jami’in dan sandan mai kula da yankin Madhubani da ke Jihar Bihar, Santosh Kumar Singh, ya ce an gurfnar da matashi Kumar ne a kotun bisa zargin yunkurin aikata fyade.

Dagacin kauyen Majhor, Nasima Khatoon, ya bayyana hukuncin kotun a matsiyin mai dimbin tarihin da zai kare martabar mata a garin.

Ya bayyana cewa matan garin na Majhor sun bayyana farin cikinsu da hukuncin.

Matan sun ce hukuncin zai ba da damar mahawara a kan laifin cin zarafin su a cikin al’umma da kuma kare martabar su.