✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kotu ta umarci DSS ta biya Sunday Igboho N20bn

Kotun ta ce samamen da DSS ta kai gidan Igbohon ya saba wa ka’ida.

Babbar Kotun Jihar Oyo a ranar Juma’a ta umarci Hukumar Tsaro ta DSS da ta biya mai ikirarin fafutukar kafa kasar Yarabawa zalla, wato Sunday Igboho Naira biliyan 20.

Alkalin kotun, Mai Shari’a Ladiran Akintola ce ta yanke hukuncin ne sakamakon karar da Igbohon ya shigar, duk da yana ci gaba da zama a tsare a Jamhuriyar Benin.

Kotun dai ta yanke hukuncin ne kan samamen da DSS ta kai gidan Igboho da ke birnin Ibadan a Jihar ta Oyo, inda ta ce hakan ya saba wa ka’ida.

Alkalin ta kuma yi fatali da sukar da aka yi tun da farko cewa kotunta bata da hurumin sauraron karar.

An dai cafke Sunday Igboho ne ranar daya ga watan Yulin 2021 a birnin Cotonou na Jamhuriyar Benin lokacin da yake yunkurin tsallakewa kasar Jamus, jim kadan bayan dirar mikiyar jami’an DSS  a gidansa da ke Ibadan.

Lauyansa, Yomi Alliu (SAN) ne dai tun da farko ya garzaya gaban kotun don kalubalantar kai samamen gidan wanda yake karewar.

Tuni dai aka saki wasu daga cikin yaran Igbohon wadanda aka kama a cikin gidan, in ban da wasu mutum biyu da ake zargi da ta’addanci.

Yanzu haka dai yana can tsare a kurkukun birnin Cotounou yana jiran a yanke masa hukunci.