✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Kotu ta tura dalibin jami’ar da ya lakada wa malamarsa duka gidan gyaran hali

“Sai da matashin ya yi mankas da kwayoyi kafin ya daki malamar.”

Wata kotun Majistare da ke Ilorin a Jihar Kwara ta tura Salaudeen Waliu, dalibin Jami’ar Ilorin da ake zargi da lakada wa wata malamarsa dukan kawo wuka, zuwa gidan gyaran hali.

Dalibin, wanda yanzu haka yake matakin aji hudu a Sashen Nazarin Kananan Halittu na jami’ar dai ana zarginsa ne da dukan malamar, mai suna Rahmat Zakariyat.

Takardar tuhumar ’yan sanda a kotun dai, ta nuna sai da matashin ya yi mankas da kwayoyi kafin ya tunkari ofishin malamar, wacce kuma ita ce mai kula da koyar sanin makamar aiki (SIWES), ta sashen da yake karatu.

Takardar ta kuma ce, “Rahotanni sun nuna ya kutsa kai cikin ofishin nata ta hanyar balle kofa ta karfin tsiya, yana mata barazanar sai ta ba shi maki a SIWES din da bai yi ba.

“Daga nan ne ya naushe ta, sannan ya yi mata dukan tsiya, har sai da ya karya tagar ofishin nata, a kokarinsa na ciro karfen da zai caka mata.

“Ihun neman taimakon da ta kwalla ne ya janyo hankalin jami’an tsaro, wadanda suka je suka ceto ta daga hannunsa”.

Da yake yanke hukunci, alkalin kotun, Mai Shari’a Muhammed Ibrahim, ya ba da umarnin a tsare matashin, sannan ya dage ci gaba da sauraron karar har zuwa ranar 26 ga watan Nuwamban 2021.