✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Kotu ta tsare matashin da ake zargi da kashe abokin fadansa ta hanyar duka

Ana tuhumarsa ne da laifin aikata kisa ta hanyar duka

Wata kotun majistare da ke Iyaganku a Jihar Oyo, ta ba da umarnin a tsare wani matashi dan shekara 22 a gidan gyaran hali na Agodi, kan zargin lakada wa abokin fadansa duka har lahira.

’Yan sandan yankin sun gurfanar da wanda ake zargin ne bisa tuhumar aikata kisa.

Akalin Kotun, Mai Shari’a Patricia Adetuyibi, ta ki amincewa da rokon wanda ake zargin kan shari’ar da ake yi masa.

Alkalin ta umarci ‘yan sanda su mayar da fayil din karar zuwa ofishin Daraktan Kararraki (DPP) don neman shawara game da shari’ar.

Daga nan, ta dage shari’ar zuwa 15 ga watan Agustan 2022 don ci gaba da shari’a.

Tun farko, lauyan mai gabatar da kara, Insfekta Salewa Hammed, ya shaida wa kotun wanda ake zargin ya aikata laifin da ake tuhumarsa ne ran shida ga watan Mayu da misalin 2:30 na dare, inda ya yi ajalin wani mai suna Dan Mallam mai shekara 23 da haihuwa.

Hammed ya ce wanda ake zargin ya yi wa marigayin dukan kawo-wuka a lokacin da ta rikice musu a garejin manyan motoci da ke Akinyele a Ibadan.

Ya ce, laifin da ya aikata din ya saba wa Sashe na 316 wanda hukuncinsa ke karkashin Sashe na 319 Dokokin Manyan Laifuka na Jihar Oyo na 2000.

(NAN)