✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Kotu ta tsare matar da ake zargi da kashe kishiyarta a Neja

Ina son ganin an bi min hakkin ’yata.

Wata Kotun Majistire da ke zamanta a birnin Minna na Jihar Neja, ta bayar da umarnin tsare matar nan da ake tuhuma da laifin kashe kishiyarta a gidan cin sarka.

Alkalin Kotun, Mai Shari’an Nasiru Mu’azu ne ya yanke hukuncin tura matar da aka gurfanar a gaban kotun a ranar Laraba tare da wasu mata uku ’yan uwanta da ake zargi sun taimaka wajen aikata laifin.

Gidan Rediyon Muryar Amurka ya ruwaito cewa, kotun ta tura su gidan kason ne domin su yi zaman jira, gabanin ta karbi shawarwari daga Ma’aikatar Shari’a ta Jihar Neja.

Yadda lamarin ya faru

A makon da ya gabata ne aka wata mata ta lakada wa kishiyarta duka da tabarya da har ya yi ajalinta sannan ta kona gawarta a Minna, babban birnin Jihar Neja.

Kishiyar tare da kannenta dauke da tabarya ne suka yi wa mamaciyar rubdugu, suka yi mata lugude, har ta bar duniya, kwana 55 da daura auren marigayiyar Fatima da mijinta.

 “Sun raba kanta biyu sannan suka sanya ta cikin daki suka banka wuta ta kone kurmus,” inji wani dan uwan marigayiyar mai suna Malam Jamilu.

Rahotanni sun bayyana cewa kishiyoyin biyu ba a gida daya suke zama ba, amma uwargidar ta yi wa marigayiya Fatima takakkiya har gida, ta yi mata bugun dawa, ta kulle ta a daki, sannan ta cinna wa gidan wuta.

Makusantanta sun bayyana cewa, “Ba a gida daya suke zama ba, amma saboda zafin kishi uwargidanta ta kai mata takakkiya har gida.”

Malam Jamilu ya ce, “Tun karfe 10 na safe zuwa daya na rana duk mun yi magana da ita.

“Amma daga karfe 3 zuwa 4 na yammci mummunan labari mai kada zuciya da hanta wanda ba zan taba mantawa da shi ba har karshen rayuwata ya same ni cewa uwargidan Fatima ta hadu da kannenta sun yi mata dukan tsiya da tabarya.”

Mun kama wacce ake zargi – ’Yan sanda

’Yan sanda a Jihar Neja sun cika hannu da matar da ake zargi da danyen aikin ne bayan ta kashe kishiyar tata ta cinna wa gawar wuta ne a ranar Talata.

Kakakin ’yan sanda a Jihar Neja, Wasiu Biodun ya ce an tsinci gawar amarya Fatima kwance cikin jini a dakinta an kona wani bangare na jikinta.

“Da muka samu rahoton, nan take muka je wurin, muka kamo kishiyarta mai shekara 24 a gidan, kuma kanwar uwargidar ce ta kashe amaryar ne da tabarya.

“An samu tabaryar a wurin da abin ya faru kuma an fara bincikar wadda ake zargin kafin a gurfanar da ita a gaban kotu,” inji shi.

Ina son a bi min hakkin ’yata – Mahaifin Amaryar

Malam Ibrahim Yahaya Sidi Na Khalifa, mahaifin amaryar da aka kashe a Talatar da ta gabata kwanaki 54 kacal da daura mata aure, ya nemi a bi masa hakkin ’yarsa da aka kashe.

A wata tattauna ta musamman tare da Aminiya, Malam Na Khalifa ya ce yana fatan shari’a za ta yi aiki ta hanyar tabbatar da cewa an hukunta wadanda suka aikata wannan danyen aiki.

A cewarsa, Musulunci ya yarda cewa babu laifi ga wanda aka zalunta kuma yanke shawarar a bi masa hakki inda ya buga hujja da yadda Alkur’ani mai girma ya yi bayani hukuncin wanda ya kashe wani ba tare da wani dalili na adalci ba.

“Ba zan taba yafe jinin ’ya ta ba don Alkur’ani ya ce babu wata rai da ta fi wata, kuma duk wanda ya kashe a kashe shi, saboda haka ina son ganin a zartar da hukunci a kan wadanda suka aikata wannan mummunan aiki.”

“A’a sam ba zan taba yafe musu ba, idan hatsari ne ko kisan kai ba da gangan ba, to wannan wani batu ne na daban.

“Amma a yi wa diya ta dukan da ya yi ajalinta, kuma ba a tsaya iyaka nan ba, sai da aka cinna wa gawarta wuta, wannan wani abu da ba zan taba yafewa ba,” a cewar mahaifin cikin zubar hawaye.

Malam Na Khalifa, ya ce labarin mutuwar ’yarsa ya zo masa da farin ciki da kuma bakin ciki a lokaci guda.

A cewarsa, farin cikin ya samo asali ne daga yakini a kan furucin Annabi Muhammmad (SAW), wanda ba ya fadin komai sai gaskiya, domin kuwa ya yi bushara da duk wanda aka kashe bisa zalunci zai dawwama a Aljanna.

“Dangane da waccan busharar, ba ni da shakkar a kan cewa ’yata za ta kasance cikin ’yan Aljanna kuma hakan a faranta min rai.”

“Sai dai kuma, na yi bakin ciki da matukar damuwa kasancewar ba zan kara ganinta ba a wannan duniyar kuma ina cikin bakin cikin tunanin abin da ta fuskanta a hannun wadanda suka kashe ta,” in ji shi.

Mahaifin ya misalta ’yarsa a matsayin mutuniyar kirki mai son zaman lafiya da kuma kyawawan dabi’u, wanda a cewarsa ta sha bamban da sauran ’yan uwanta ta fuskar kyawun halayya.

Ya ce duk da cewa ba shi da kudin da zai iya daukaka karar, amma ya yi murna da jin cewa Sarkin Minna ya sa hannu a lamarin kuma wasu kungiyoyin kare hakkin dan Adam sun suna sha’awarsu domin ci gaba da ganin adalci ya tabbata har zuwa karshen lamarin.