✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kotu ta tsare masu shaye-shaye da buga ludo a masallaci a Kano

An zargi mutanen hudu da mayar da masallaci wajen shaye-shayensu.

Kotun Musulunci a Jihar Kano ta tsare wasu mutum hudu a gidan yari kan zargin yin da shaye-shaye da kuma buga ludo a cikin wani masallaci.

Kotun Musulunci da ke unguwar PRP a Gama a Karamar Hukumar Nassarawa ta ba da umarnin ne bayan an gurfanar da mutanen wadanda duk mazauna unguwar Rimin Kebe ne.

Tun da farko wani Auwalu Usman ne ya yi karar cewa mutanen hudu sun hada baki suna shiga masallaci domin yin wasan ludo da kuma shaye-shaye.

Ya ce yayin da ya yi yunkurin hana su, sai suka taru suka yi masa dukan tsiya tare da yi masa barazana cewa ya yi musu katsa-landan a harkokinsu.

Wanda ake kara na farko ya amince da laifin da ake tuhumar sa, yayin da sauran ukun suka musanta zargin da ake yi musu a lokacin da mai gabatar da kara, Aliyu Abidin Murtala ya karanta musu tuhume-tuhumen.

Alkalin kotun, Malam Nura Yusuf Ahmed, ya bayar da umarnin ci gaba da tsare su a gidan gyaran hali har zuwa ranar 3 ga watan Janairun 2024, domin gabatar da shaidu a gaban kotu.