Wata kotun yanki da ke Karu a yankin Babban Birnin Tarayya Abuja ta tsare wani mai gadi mai suna Polycarp Ugeme, a gidan gyaran hali bisa laifin daba wa makwabcinsa wuka a baya.
Alkalin kotun, Ishaq Hassan, ya bayar da umarnin a ci gaba da tsare wanda ake tuhuma har zuwa ranar 19 ga watan Janairu domin tantance hukuncin da zai yanke masa.
- Muna da hujjoji kan cewa Tinubu tsohon mai laifi ne – Dino Melaye
- Gwamnati ce ta lalata harkar fim – Abba Al-Mustapha
Ana tuhumar Polycarp, wanda mazaunin Jikwoyi, a Abuja ne bisa laifin yi wa makwabcinsa rauni, wanda kuma tuni ya amsa laifin nasa.
Lauyan masu gabatar da kara, Olarewaju Osho ya shaida wa kotun cewa wanda ya shigar da kara, Uche Augustine ne, ya kai rahoton faruwar lamarin a ofishin ‘yan sanda na Jikwoyi a ranar 10 ga watan Janairu.
A cewarsa, wanda ya shigar da karar ya yi zargin cewa ya bi wani abokinsa ne domin karbar kudi na wani aiki da ya yi, wanda kan haka ne wanda ake karar ya kai masa hari.
Ya ce ana cikin haka ne wanda ake zargin ya zare wuka daga aljihunsa ya daba wa mai karar a bayansa har sau uku kafin a garzaya da shi asibiti.
Osho ya ce an kai wanda aka yi wa raunin asibiti inda yake ci gaba da jinya.
Laifin dai ya ci karo da sashe na 240 na kundin laifuffuka.