✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kotu ta tattabatar wa Abba Yusuf takarar Gwamnan Kano a PDP

Babbar Kotun Jihar Kano ta 3 a karkashin Mai shari’a A.T. Badamasi ta kori karar da Alhaji Jafar Sani Bello ya shigar gabanta, inda ya…

Babbar Kotun Jihar Kano ta 3 a karkashin Mai shari’a A.T. Badamasi ta kori karar da Alhaji Jafar Sani Bello ya shigar gabanta, inda ya ke kalubalantar dan takarar Gwamnan Jihar Kano a karkashin Jam’iyyar PDP, Alhaji Abba K. Yusuf da jam’iyyar da kuma Hukumar Zabe  tab Kasa (INEC) cewa an gudanar da zaben fitar da gwani na jam’iyyar ba bisa ka’ida ba.

Mai karar ya yi korafin cewa wanda PDP ta tsayar takara wato Abba K. Yusuf bai cika sharuudan yin takara a jam’iyyar ba, don haka ya roki kotun ta soke zaben fid-da- gwani da aka yi a baya tare da ayyana shi a matsyain halattaccen dan takarar Gwamna a PDP..

Sai dai Lauyan wanda ake kara, Barista Bashir Tudun Wazirci ya roki kotun ta kori karar saboda an bi dukan sharuddan da ake bukata a zaben fitar da gwanin.

Da yake yanke hukunci, Mai shari’a A.T. Badamasi ya bayyana cewa banagaren masu karar sun gaza gabatar wa kotu kwararan hujjoji kan zarginsu, don haka kotun ta yi watsi da bukatarsu.

Lauyan wanda ake kara ya bayyana gamsuwa da hukuncin da kotun ta yanke.

Sai dai mai karar Jafar Sani Bello ya bayyana cewa bai yarda da wancan hukunci da kotun ta yanke ba, don haka a saninsa har yanzu shi ne dan takarar Gwamna na PDP.

Ya kara da cewa zai zauna da lauyoyinsa domin daukar mataki na gaba.