✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kotu ta soke hukuncin hana PDP takarar Gwamnan Zamfara

Da farko Babbar Kotun Tarayya da ke Gusau, ta soke zaben Dauda Lawan a matsayin dan takarar Gwamna Jihar Zamfara a PDP

Kotun Daukaka Kara ta soke Hukuncin Babbar Kotun Tarayya da ta haramta wa Jam’iyyar PDP shiga zaben Gwamnan Jihar Zamfara a 2023.

Kotun Daukaka karar da ke zamanta a Sakkwato ta soke hukuncin da a baya ya soke takarar Dauda Lawal Dare wanda PDP ta gabatar a matsayin dan takarar gwamnan Zamfara a zaben da ke tafe a watan Maris.

Hukucin na ranar Juma’a na zuwa ne bayan da farko Babbar Kotun Tarayya da ke Gusau, ta soke zaben dan takarar Gwamna Jihar Zamfara da PDP ta gudanar, wanda Dauda Lawal ya lashe.

Rikicin zaben tsayar da dan takarar Gwamnan Zamfara a PDP ne dai ya fara kai masu neman takarar zuwa kotu, inda ta soke zaben ta sa a gudanar da sabo.

A zaben fid-da-gwanin da PDP ta gudanar ranar 25 ga watan Mayu, 2022, Dauda Lawal ya samu kuri’a 431, wanda ya ba shi damar zama dan takarar gwamnan Zamfara a inuwar jam’iyyar.

Tun da farko, ’yan takara uku a zaben — Abubakar Nakwada, Wadatau Madawaki da kuma Ibrahim Shehu-Gusau — sun janye daga zaben saboda abin da suka kira rashin bin ka’ida.

Daga bisani a watan Yuni, Shehu-Gusau, Madawaki da kuma Aliyu Hafiz Muhammad — shi ma mai neman takara — suka garzaya kotu suna neman a soke zaben da Dauda Lawal a lashe a matsayin dan akarar gwamnan Zamfara a Jam’iar PDP, saboda abin da suka kira saba kundin tsarin jam’iyyar.

Sai dai daga bisani, alkalin a wani zama na daban ya soke zabe dan takarar da PDP ta gudanar tare da haramta mata tsayar da dan takarar Gwamnan Jihar Zamfara a zaben 2023.

Amma daga bisani a ranar Juma’a kotun daukaka kara da ke zamanta a kotu ta soke hukuncin babbar kotun.