✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Kotu ta sake tisa keyar Sowore zuwa gidan yari

Ana zargin sa da shirya manakisa da harzuka jama'a da kuma shirya haramtaccen taro

Kotu ta tsare jagoran zanga-zangar #RevolutionNow kuma mamallakin jaridar intanet ta Sahara Reporters, Omoyele Sowore da wasu mutun hudu a Gidan Yarin Kuje da ke Abuja.

Kotun Majistare da ke zamanta a Wuse, Abuja, ta bayar da umarnin ne yayi sauraron shari’ar zargin su da shirya makarkashiya, gudanar da haramtaccen taro da kuma neman harzuwa jama’a, amma sun musanta zargin.

“An tura mu Gidan Yarin Kuje na tsawon awa 24 yayin da suke shirin daukar mataki na gaba,” kamar yadda Sowore ya wallafa a shafinsa na Twitter.

Alkain kotun, Mabel Segun Bello, ta ce a ci gaba da tsare Sowore da sauran mutum hudun ne har sai ta kammala sauraron bukatarsu ta samun beli.

Kotun da kuma sanya ranar Talata, 5 ga watan janairun 2021 don sauraron bukatar tasu ta samun beli wanda lauyansu, Mashal Abubakar zai gabatar.

An tsare su ne a ranar 31 ga watan Disamba, 2020 a Abuja, a lokacin da suke gudanar da zanga-zangar rashin amince da abin da suka kira rashi shugabanci na gari, aka kuma kai su caji ofis.