Kotun Sauraron Kararrakin Zabe a Jihar Kano ta soke nasarar da dan Majalisar Tarayya mai wakiltar kananan hukumomin Kura da Madobi da Garun Malam, Yusuf Umar Datti na jam’iyyar NNPP ya samu.
Alkalan kotun guda uku da ke karkashin jagorancin Mai Shari’a Ngozi Flora Azinge, ta ce Yusuf Datti bai cancanci tsayawa takara ba saboda bai ajiye aikinsa na Jami’ar Bayero ba kwanaki 30 gabanin zabe.
- Tinubu zai zarce Dubai daga India
- Likitan da ake zargi da yanke ƙodar mara lafiya ya koma ‘mahaukaci’ a ofishin ’yan sanda
Kan haka ne kotun ta ce ta soke nasarar da Datti ya samu tare da wofantar da shaidar lashe zabe da Hukumar Zabe ta Kasa INEC ta danka masa, inda ta ayyana Musa Iliyasu Kwankwaso na jam’iyyar APC a matsayin wanda ya yi nasara.
Mai Shari’a a Azinge ta umarci INEC da ta bai wa Musa Iliyasu Kwankwaso shaidar lashe zabe la’akari da cewa shi ne ya zo na biyu a yayin zaben da aka gudanar a ranar 25 ga watan Fabraiirun 2023.
Kazalika, kotun ta kuma tabbatar da nasarar da Injiniya Sani Bala Tsanyawa na jam’iyyar APC a matsayin dan majalisar mai wakiltar kananan hukumomin Kunci da Tsanyawa a Tarayya.
Kotun ta yi watsi da zargin saba wa Dokar Zabe ta 2022 a karar da Abdullahi Safiyanu Muhammad na jam’iyyar NNPP ya shigar yana kalubalantar nasarar Inijiya Tsanyawa.
Mai Shari’a Azinge ta ce dan takarar jam’iyyar ta NNPP ya gaza gamsar da kotun da kwararan hujjoji da ke nuna an samu gibi wajen yi wa Dokar Zabe da a rumfunan zabe na 1 da na 2 da na 3 da ya yi zargi.
Aminiya ta ruwaito yadda a bayan nan Kotun Sauraron Kararrakin Zabe a Jihar Kano ta soke nasarar da dan Majalisar Tarayya mai wakiltar Karamar Hukumar Tarauni, Mukhtar Yarima na jam’iyyar NNPP ya samu.
Kotun dai ta ce ta soke zaben ne saboda zargin badakakar takardun karatun dan majalisar.
Dan takarar jam’iyyar APC, kuma tsohon dan majalisar mazabar, Hafizu Kawu ne ya kai karar yana kalubalantar sahihancin takardun na Yarima.
Alkalan kotun guda uku da ke karkasjin jagorancin Mai Shari’a I.P. Chima, ta ce Yarima bai cancanci tsayawa takara ba saboda ya gabatar da sakamakon kammala Firamare ta bogi.