✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Kotu ta sake dage shari’ar Nnamdi Kanu

An bai wa lauyoyin Nnamdi Kanu damar yin nazari kan sababbin tuhume-tuhume 15 da aka shigar a kansa.

Babbar Kotun Tarayya da ke zamanta a Abuja ta dage ci gaba da shari’ar Nnamdi Kanu, jagoran IPOB, kungiyar ’yan aware masu fafutikar kafa kasar Biyafara.

Kotun ta ce ta dage shari’ar zuwa Laraba don bai wa lauyoyin da ke kare Nnamdi Kanu damar yin nazari kan sababbin tuhume-tuhume 15 da GwamnatinTarayya ta shigar a kansa.

Sai dai Nnamdi Kanu bai ce ya amince da tuhume-tuhumen ba kuma bai ce bai amince da su ba bayan an karanto masa su.

Lauyoyinsa sun shaida wa kotun cewa wanda suke karewa ba zai iya cewa komai ba har sai sun yi nazarin tuhume-tuhumen.

A jiya Litinin ne Gwamnatin ta sake gabatar da sababbin tuhume-tuhume har guda 15 kan Nnamdi Kanu, kari a kan guda bakwai da tun da farko aka gabatar masa.

Bayanai sun ce wannan da shi ne karo na biyu da gwamnatin ke yin kwaskwarima a kan tuhume-tuhumen da ta shigar a kan jagoran na IPOB.
Nnamdi Kanu zai sake gurfana a kotun Abuja, bisa tuhumar cin amanar kasa da ta’addanci, da kafa haramtacciyar kungiya, laifukan da hukuncinsu kisa ne idan sun tabbata.