✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kotu ta sake ba da umarnin cafke Dan Sarauniya

Kotun ta bayar da umarnin kama Dan Sarauaniya nan take.

Kotun Majistare mai lamba 58 da ke zamanta a unguwar Nomansland a birnin Kano, ta soke belin da ta bayar ga tsohon Kwamishinan Ayyuka na Jihar Kano, Injiniya Mu’azu Magaji wanda aka fi sani da Dan Sarauniya.

Kotun karkashin jagorancin Mai shari’a, Aminu Gabari ta yanke wannan hukuncin ne kan rashin halartar zamanta har sau 3 domin amsa tuhumar da ake masa na bata sunan Gwamnan Jihar Kano, Dokta Abdullahi Umar Ganduje.

Haka kuma kotun ta bayar da umarnin kama shi tare da mika sammaci ga mutane biyun da su tsaya masa da su bayyana a kotun ranar 28 ga Maris 2022.

Sai dai lauyan Dan Sarauniya, Barista Garzali Datti Ahmad ya bayyana cewa a yanzu haka suna kokarin ganin kotun ta janye wancan umarni da ta yi.

“Abin da ya faru shi ne an nemi mu je kotu ranar Juma’a da ta gabata.

“Sai dai lokacin da muka je har yamma Alkali bai zauna ba don haka Magatakardan kotun ya ce mu dawo ranar Litinin.

“Amma duba da cewa akwai taron lauyoyi a ranar Litinin ya sa aka nemi mu zo kotun a ranar amma bayan sun tashi taro misalin karfe biyu na rana.

“Sai dai a ranar Litinin din da muka je kotun sai muke samun wannan labari.

“Hakan ya sa muka je wurin Alkalin inda muka yi masa korafi ankan hakan.

“Bayan Alkalin ya tabbatar da abin da muka fadi daga Magatakardan kotun sai ya umarci mu je mu rubuta takardar neman kotu ta janye wancan umarni mu kai Ma’aikatar Shari’a,” a cewar Barista Garzali Datti.