✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Kotu ta sa ranar sauraron korafin tsige Matawalle

Wasu mambobi PDP biyu na neman kotu ta sauke Matawalle daga kujerarsa.

Wata Babbar Kotun Tarayya da ke zamanta a Abuja, ta sanya 16 ga watan Yulin bana, a matsayin ranar da za a fara zaman sauraron korafin da ke kalubalantar sauyin shekar Gwamna Bello Matawalle na Jihar Zamfara, daga jam’iyyar PDP zuwa APC.

Mai shari’a Inyanga Ekwo ne ya sanya ranar bayan sauraron korafin bangaren da ke wakiltar masu kalubalantar gwamnan da kuma na masu kare shi.

Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya NAN ya ruwaito cewa, wasu mambobin jam’iyyar PDP biyu daga Jihar Zamfara suke kalubalantar matakin.

Bayanai sun ce Sani Kaura Ahmed da Abubakar Muhammad ne suka nemi kotun ta tsige gwamnan kan sauyin shekara a cikin korafin da suka gabatar mata mai lamba FHC/ABJ/CS/489/2021.

Aminiya ta ruwaito cewa, tun a karshen watan Yunin da ya gabata ne Gwamnan ya sauya sheka daga jam’iyyar PDP zuwa APC.

Sai dai sauyin shekar ya yamutsa hazo a yayin da wasu musamman jam’iyyyar PDP ke ganin bai cancanci ci gaba da zama a matsayin gwamna ba.

PDP ta ce ita kotu ta tabbatar da bai wa akalar jagoranci biyo bayan dambarwar siyasa da ta dabaibaye jihar Zamfara a yayin babban zaben kasa na 2019.