✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kotu ta sa ranar bayyana huruminta kan rushe masarautun Kano

Kotun za ta fayyace ko tana da hurumin sauraron ƙarar rushe masarautu biyar a jihar Kano.

Babbar Kotun Tarayya da ke Kano ta sanya ranar 13 ga watan nan na Yuni domin bayyana hukuncinta a kan takaddanar da ke gabanta ta rushe masarautu biyar a jihar.

Ana sa ran kotun za ta fayyace ko tana da hurumin sauraron ƙarar da aka shigar gabanta kan rushe masarautu biyar a jihar ko kuma ba ta da hurumi.

Tun da farko kotun ta bukaci bangarorin biyu su yi mata bayani kan ko tana da hurumin ko kuma akasin haka, inda kowanne bangare ya yi bayani tare da kafa hujjoji da irin shari’o’in da suka gabata kan rikicin masarautu a ƙasar.

Lauyan ɓangaren gwamnatin Kano ya shaida wa kotun cewa wanda ya shigar da karar ma ba shi da hurumin neman kare masa hakki saboda dokar da ta ba shi damar zama ɗan majalisar sarki an rushe ta.

To amma lauyan mai ƙara ya ƙalubalanci hakan da cewa, idan ana batu na take haƙƙin ɗan Adam to al’amari ne da ba shi da iyaka don haka kotun ta ci gaba da sauraron wannan shari’a.

Bayan sauraren doguwar muhawarar daga dukkanin ɓangarori biyu, Alƙalin Kotun Abdullahi Muhammad Liman, ya sanar da ranar da kotun za ta yanke hukunci kan wannan batu.

Ana iya tuna cewa, Sarkin Dawaki Babba na Masarautar Kano, Aminu Babba Dan Agundi ya shigar da kara kotun yana neman a yi wa Gwamnatin Kano shamaki daga rushe dokar da ta kafa masarautu biyar a jihar.