Babbar Kotun Tarayya ta yi watsi da bukatar Jam’iyyar APC na hana gudanar da zaben kanann hukumomin Jihar Kano.
APC da Hon. Aminu Aliyu Tiga sun shigar da karar ne gaban Mai Shari’a Simon Amobeda, suna neman umarnin hana hukumar zaben Kano (KANSIEC) da majalisar dokoki da kwamishinan shari’an jihar da wasu mutane 11 gudanar da zaben a kananan hukumomi 44 da ke fadin Jihar Kano.
Mai shari’a Amobeda ya ki amincewa da bukatar APC na dakatar da hukumar daga ci gaba da shirye-shiryen zaben da aka shirya gudanarwa ranar 26 ga Oktoba, 2024.
Alkalin ya dage ci gaba da sauraron karar zuwa ranar 4 ga watan Oktoba 2024 tare da jan kunnen bangarorin da su guji duk wani mataki da zai hana sauraron sauraren karar da kuma gaggauta yanke hukunci.