✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kotu ta jingine dokar rushe masarautun Kano

Ta sake jaddada umarnin kowane ɓangare ya tsaya a matsayarsa har zuwa hukuncin da ta yanke a gaba.

Babbar Kotun Tarayya ta jingine sabuwar dokar da Gwamnatin Kano ta yi amfani da ita wajen rushe masarautun Kano biyar da aka ƙirƙiro a 2019.

Ana iya tuna cewa a watan Mayun da ya gabata ne dai Majalisar Dokokin Kano ta yi ƙudirin dokar rushe masarautun Kano biyar, inda kuma ba tare da ɓata lokaci ba Gwamna Abba Kabir Yusuf ya sanya hannu ta zama doka.

Bisa dokar ne gwamnan ya rushe sarakunan biyar ciki har da Alhaji Aminu Ado Bayero ya kuma sake naɗa Muhammadu Sanusi II a matsayin Sarki na 16, bayan da tsohon Gwamnan Kano, Abdullahi Umar Ganduje ya tuɓe a 2020.

To sai da kuma a ranar 23 ga watan na Mayu ne ɗaya daga cikin masu naɗa Sarkin Kano, Alhaji Aminu Babba Ɗan Agundi mai sarautar Sarkin Dawaki Babba ya ƙalubalanci dokar a Babbar Kotun Tarayyar da ke Kano, inda ya nemi alƙalin da ya ayyana dokar a matsayin haramtacciya.

A yayin zaman kotun na yau Alhamis, kotun ta rushe duk wasu tanade-tanade da Gwamnatin Kano ta yi amfani da su wajen rushen dokar

Mai Shari’a Abdullahi Muhammad Liman wanda ya yanke hukuncin ya bayyana cewa, Gwamnatin Kano ta bijire wa umarnin da ya nemi da ta dakata da kafa sabuwar dokar amma ta biris inda ta yi gaban kanta

Alƙalin ya ce Kotun za ta yi amfani da ikonta wajen tilasta kiyaye duk wani umarni da ta gindaya.

Sai dai kotun ta ce umarnin da ta bayar a baya na kowanne ɓangare ya tsaya a matsayarsa — tsakanin masu ƙara da waɗanda ake ƙara — yana nan babu abin da ya sauya.

Haka kuma, kotun ta ƙi amincewa da buƙatar da aka gabatar na neman ta ayyana dokar da ta rushe masarautun a matsayin haramtacciya ko akasin haka.

Aminiya ta ruwaito cewa, a ƙarshe kotun ta miƙa wannan taƙaddama a hannun Mai Shari’a Simon Amobeda la’akari da ɗaga likafarsa zuwa Kotun Daukaka Kara domin ci gaba da sauraron ƙarar.