Babbar Kotun Jihar ta hana Babban Bankin Nijeriya (CBN) da Gwmanatin Tarayya riƙe kuɗaɗen ƙananan hukumomin jihar 44 na wata-wata.
Kotun ta bayar da umarnin wucin gadin ne ga Gwamantin Tarayya da hukumominda ma’aikatunta, bayan ƙarar da Ƙungiyar Ma’aikatan Ƙananan Hukumomi ta Nijeriya (NULGE) da wasu masu kishin Jihar Kano.
Alƙalin kotun, Mai Shari’a Ibrahim Musa Muhammad, ya ba da umarnin ne ga CBN da Hukumar Rabon Kudaden Shiga na Kasa da Kuma Akanta-Janar na Tarayya kan tabawa, rikewa ko jinkirin sakin kudaden kananan hukumomin na jihar Kano.
Ya ba da umarnin ne kan karar da masu karar suka nuna damuwa cewa game da yiwuwar rikewa ko jinkirin kudaden kananan hukumomin ko wani bangaren kudaden.
Alkalin ya kuma umarci hukukumomin gwamantin da wakilansu da kada su kuskura su yi duk wani nau’in katsalandan kan kudaden kananan hukumomin.
Daga nan ya dage zaman zuw ranar 21 ga watan nan na Nuwamba, 2024.