Babbar Kotun Tarayya ta yanke hukuncin daurin shekara shida ga George Turnah, yaron gidan tsohon shugaban kasa Goodluck Jothanan, da abokan cin mushensa, kan laifin damfara ta Naira biliyan 2.9.
Kotun da ke zamanta a Fatakawal, Jihar Ribas ta daure George Turnah ne a ranar Alhamis tare da Ebis Orubebe and Uzorgor Silas Chidebere da wasu kamfanoni, bayan da ta same su da laifin yaudara, amfani da takardun bogi, safarar kudaden haram, da kuma ci da gumin wani.
- Gwamnatin Sojin Nijar ta tsige shugaban ’yan sandan Yamai
- Kannywood: Gwamnatin Kano ta rufe gidajen kallo da masu ‘downloading’
A shekarar 2017 Hukumar Yaki da Masu Karya Tattalin Arziki (EFCC) ta fara gurfanar da su, ciki har da George Turna, tsohon hadimin tsohon Shugaban Hukumar Neja Delta (NDDC), Dan Abia, kan zargin damfara ta Naira biliyan 2.89.
Mai Shari’a A.T Mohammed ya same su da lafin hada baki da wasu kamfanoni suka karbi kudade a 2014 daga hukumar NDDC, da sunan za us samar da ayyukan yi ga kungiyoyin matasa da mata 300.
Sannan caji na 23 ya ce, “George Turnah ya karbi Dala miliyan daya (a kan canjin Dala N184)” daga wani dan canji ba bisa ka’ida ba.
Daga bisani Mai Shari’a A.T Mohammed ya yanke wa kowannensu hukuncin daurin shekara biyu a gidan yari, daga ranar da aka tsare shi, ko biyan tara
Akalin ya ba wa Turnah zabin biyan tarar Naira miliyan daya, sauran kuma N500,o00 kowannensu; wadanda ake zargi na 4, 6 da 10 kuma za su mayar da N180,000,000 asususun gwamnati na bai daya.
Turnah zai biya hukumar NDDC N5,000,000, masu lafi na 4 da na 10 kuma za su biya ta N100,000,000da.
Akwai kuma N46,760,843.61 da mai laifi na 9 zai biya NDDC, mai laifi na 4 zai ba ta N494,371.86, mai laifi na biyu ya biya ta N13,000,000 sai mai laifi na uku da zai biya ta N23, 500,000.