✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Kotu ta daure wanda ya lalata karamar yarinya shekara bakwai

Kotun ta yanke wa mai shekara 40 hukuncin daurin shekara bakwai saboda fyade

Wata Babbar Kotu da ke zamanta a Uyo, Jihar Akwa Ibom, ta yanke wa wani mai shekara 40 hukuncin daurin shekara bakwai a kurkuru saboda laifin yi wa karamar yarinya fyade.

Mutumin wandadan kasuwa ne daga jihar Abia, ya far wa yarinyar mai shekara 12 ne bayan ya yaudare ta ta je gidansa karbar kudin kayan da ya saya a wurinta a ranar 2 ga watan Fabrairu, 2018.

Yarinyar ta shaida wa kotun cewa mutumin ya sayi kayan marmari na Naira N130 a wurinta sannan ya ce ta bi shi gidansa ta karbi kudinta.

Da ta isa gidan, sai ya yi ta mata maganganun da basu kamata ba da kokarin koya mata badala tun wurin karfe takwas na dare har zuwa tsakar dare.

Bayan wanda ake tuhumar ya kasa kare kansa daga zargin, ya nemi ya tsare daga kotun ta hanyar neman a ba shi dama yana son kama ruwa.

Kotun karkashin Mai Shari’a Okon Okon ta kama shi da laifin yi fyade ta karamar yarinya daliba ‘yar aji daya a sakandire.

Ta kuma yanke zartar masa hukuncin laifin zakke wa karamar yarinya, dadidai da tsarin hukunta masu aikata fyade na kundin tsarin dokar jihar.