Wata kotun musamman da ke zamanta a Ikejan Jihar Legas ta yanke wa wani sojan karya mai mukamin Janar hukuncin daurin shekara bakwai saboda kwaikwayon sa hannun Shugaba Buhari wajen yin damfarar Naira miliyan 266.
Kotun dai ta sami Janar Bolarinwa Abiodun, wanda asalin sunansa shi ne Hassan Ayinde, ne da laifin saboda yin sojan gona a matsayin Babban Hafsan Sojojin Kasa na Najeriya wajen aikata damfarar.
- An maka APC a kotu kan yunkurin sauya sunan Mataimakin Tinubu
- Munanan hare-hare 12 da aka taba kai wa gidajen yari a Najeriya
Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya (NAN) ya rawaito cewa wanda ake zargin ya amsa laifuka 13 da aka zarge shi da aikatawa masu alaka da samun kudi ta haramtacciyar hanya, yin sojan gona da kuma aikata damfara.
Tun farko hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta EFCC ce ta gurfanar da shi a gaban kotun.
Da take yanke hukunci ranar Alhamis, Alkalin kotun, Mai Shari’a Oluwatoyin Taiwo, ta aike da wanda aka samu da aikata laifin gidan gyaran halin ba tare da zabin biyan tara ba.
Ta ce, “Wanda ake karar ya bayyana kansa a matsayin Janar na soja, wanda ya kwaikwayi sa-hannun tsohon Shugaban Kasa Olusegun Obasanjo, da na yanzu, Muhammadu Buhari, sannan ya damfari mutane da sunansu.
“Ya yi amfani da kwarewa sosai wajen aikata damfarar, ta yadda mutane za su yi tunanin ta yaya zai iya kubuta? Wannan abin takaici ne yadda irin wadannan mutanen ke bata wa kasarmu suna.
“Saboda haka, na yanke masa hukuncin daurin shekara bakwai a gidan gyaran hali ba tare da zabin tara ba.
“Kazalika, zai biya wanda ya damfara din Naira miliyan 20, sannan mun umarci a rufe asusun ajiyarsa na bankin First Bank da ya yi amfani da shi wajen aikata damfarar.
“Sannan mun kwace gidansa da ke lamba daya kan titin Joke Ayo a Alagbado, da kuma motocinsa guda hudu; bakar Range Rover da bakar BMW da bakar Toyota Land Cruiser da kuma farar Toyota Hilux mai lamba Lagos KTU 985 ET,” inji alkalin. (NAN)