Kotun Shari’ar Musulunci da ke zamanta a Unguwar Kwana Hudu da ke Jihar Kano, ta yanke wa wani matashi hukuncin daurin watanni 6 a gidan gyaran hali bisa samunsa da karya kafar wani dan sanda.
Tun da farko an tuhumi matashin mai suna Umar Usaini Birnin Kudu da laifin karya kafar wani jami’in dan sanda a Karamar Hukumar Takai ta Jihar Kano.
- Buhari ya gana da Emefiele bayan hukuncin Kotun Koli
- Buhari zai tsawaita wa’adin tsofaffin kudi zuwa watan Afrilu
Lamarin ya faru ne yayin da jami’in dan sandan ya ziyarci matashin domin sanar da shi cewa an yi korafi a kansa a ofishin ’yan sanda na garin Takai.
Wakiliyarmu ta ruwaito cewa, matashin ya karya karfa dan sandan guda daya yayin da yake kokarin guduwa.
Bayan cafke shi ne aka gurfanar da shi a gaban kotun inda kuma ya amsa zargin da ake yi masa.
Mai gabatar da kara a gaban kotun, Aliyu Abidin Murtala ya roki kotun da ta yi masa hukunci bisa ikirarin bakinsa.
Alkalin kotun, mai shari’a Mallam Nura Yusuf Ahmad, ya yanke masa daurin watanni 6 a gidan gyaran hali ba tare da zabin biyan tara ba.
Kazalika, kotun ta yanke cewa matashin zai biya kudin dori da magani har Naira dubu dari da arba’in da uku da dari biyar.