✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kotu ta daure matashi wata 4 kan satar doya

An gano matashin ya saci doyar ne a wata makaranta.

Wata kotu da ke unguwar Dei-Dei a Abuja ta yanke wa wani matashi dan shekara 22 hukuncin daurin wata hudu a gidan gyaran hali kan laifin satar doya a wata gona.

An tuhumi Adams wanda ba shi da laifin zamba da kuma sata.

Lauyan mai gabatar da kara, Mista Chinedu Ogada, ya shaida wa kotun cewa wanda ake tuhuma ya aikata laifin ne a ranar 19 ga watan Oktoba, 2023.

Ogada ya ce, ’yan sandan da ke sintiri karkashin jagorancin Mista Tonushi Chibwa ne suka kama wanda ake tuhumar a tashar Dutsen Alhaji.

Ya ce a wannan ranar da misalin karfe 10 na dare rundunar ta kama mai laifin tare da wata tarin doya da ake zargin na sata ne.

Mai gabatar da kara ya bayyana cewa, a lokacin da ’yan sanda suka gudanar da bincike sun gano cewar matashin ya sato doyar ce a wata gona da ke makarantar sakandare ta gwamnati a Dutse Alhaji.

Ya shaida wa kotun cewa wanda aka yanke wa hukuncin ya ce ya saci doyar da nufin sayarwta amma ana cikin haka ne aka kama shi.

Ogada ya ce laifin ya ci karo da tanadin sashe na 348 da na 287 na kundin laifuffuka.

Alkalin kotun, Jastis Saminu Suleiman, ya yanke wa wanda ake kara hukuncin zaman gidan yari na tsawon wata hudu tare da biyan tarar Naira 10,000.

Alkalin ya gargade shi da ya guji aikata laifi mai alaka da hakan a nan gaba.