✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kotu ta daure matashi saboda yada labarin karya a kan COVID-19

Kotun ta daure shi ne bayan hukumar DSS ta kai karar shi

Wata kotun majistare a Jihar Kogi, ta daure wani mai suna Habibi Rabiu wata biyu a kurkuku bayan da ta kama shi da laifin wallafa bayanin karya a shafinsa na Facebook kan cutar COVID-19.

An dai sami mutumin ne da yada labarin karya a kan cutar COVID-19 a shafin nasa na Facebook.

Hukumar tsaro ta DSS ce ta cafke Rabi’u kana ta gurfanar da shi a kotun kan wani bayani da ya wallafa a shafin Facebook dinsa mai taken, “Abin damuwa ne yadda zazzabi ke kashe mutane a Jihar Kogi.”

Rahotanni sun ce mai laifin ya wallafa bayanin a shafin nasa ne tun a lokacin da dokar kulle ta COVID-19 ke da zafi-zafinta a kasar nan.

Lauyan masu gabatar da kara, M. A. Abaji, ya fada wa kotu cewa laifin da mai kare kansa ya aikata ya saba wa sashe na 393 na Final Kod na Jihar Kogi wanda ya danganci jefa tsoro a zukatan ’yan Jihar da kuma neman gwara kansu da gwamnati.

Shi kuwa lauya mai kare wanda ake tuhuma, E .A. Iwu, ya ce wanda yake karewa ya aikata haka ne daidai da abinda ya faru ga wata ’yar uwarsa, wadda ta rasa ranta a Jihar saboda zazzabin maleriya.

Bayan ta saurari duka bangarorin, alkalin kotun, Mai Shari’a A.A. Agatha, ta yanke wa mutumin hukuncin daurin wata biyu a gidan yari ba tare da zabin biyan tara ba, har da Karin biyan kudi Naira dubu biyar kamar yadda doka ta tanadar.