Wata kotun Majistare mai zamanta a Yaba, Jihar Legas, ta yanke wa wani jami’in banki, Omosanyin Eniola hukuncin daurin shekara bakwai a gidan yari bayan da ta kama shi da laifin magudin kudi har N21.8m.
Kotun, karkashin Alkalin Linda Yetunde Balogun, ta daure mai laifin ne bayan da ta same shi da aikata biyu daga cikin laifuka bakwai da aka tuhume shi da su.
- Ba ni da niyyar sake mayar da babban birnin Najeriya zuwa Legas idan na ci zabe – Tinubu
- ‘Har yanzu aniyar Buhari ta cire ’yan Najeriya 100m daga kangin talauci tana nan daram’
’Yan sanda sun tuhumi ma’aikacin bankin da hadin baki, magudi da kuma satar takardun cire kudi a bankin.
Alkalin kotun ya ce, mai gabatar da kara ya gabatar wa kotun gamsassun hujjoji a kan wanda ake zargi, wanda hakan ya sa kotun ta daure shi shekara bakawai a gidan gyaran hali.
Sai dai, kotun ta wanke mai laifin daga sauran zarge-zargen da ta ce ba ta gamsu da hujjojin da aka gabatar mata a kansu ba.