✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gobara ta yi ajalin jami’in Kwastam da Iyalansa 5 a Osun

Jami'in da iyalinsa biyar sun rasu nan take.

Wani Jami’in Hukumar Kwatsam mai suna, Tijjani Kabiru da matarsa da yaransa huɗu sun rasu sakamakon tashin gobara a gidansu da ke unguwar Akankan, Ede, a Jihar Osun.

Gobarar ta tashi ne da misalin ƙarfe 3 na dare, inda ta ƙone gidan gaba ɗaya, sai dai wani yaro ɗan shekara 13 ya tsallake rijiya da baya.

Hukumar Kashe Gobara ta Jihar Osun, ta tabbatar da faruwar lamarin a wata sanarwa da Daraktan Hukumar, Mista Olaniyi Alimi, ya fitar, wacce kakakin hukumar, Ibrahim Adekunle, ya raba wa manema labarai.

“Muna samun kiran gaggawa da misalin ƙarfe 3:21 na dare, nan take muka tura tawagarmu daga ofishin Ede, tare da ƙarin wata tawaga daga Hedikwatar Hukumar a Abere,” in ji sanarwar.

Gidan ya kama da wuta, lamarin da ya yi sanadin mutuwar Kabiru, wanda ake tsammanin yana da shekaru 40, matarsa mai shekara 40 a duniya sun rasu.

Har ila yau, yaransu huɗu, maza uku da mace ɗaya, waɗanda shekarunsu daga uku zuwa 10 ne duk sun rasu.

Aƙalla kayan Naira miliyan 200 ne suka ƙone a lokacin gobarar, amma an yi nasarar ciro wasu kayayyaki a gidan.

Hukumar ta bayyana cewar tana ci gaba da bincike don gano musabbabin tashin gobarar.