Wata kotu a yankin Lugbe da ke Abuja ta yanke wa Terkaa Akishi mai shekaru 36 hukuncin ɗaurin watanni goma sha biyar a gidan gyaran hali saboda satar Alqur’anai.
Alƙalin kotun, Malam Aliyu Kagarko ya daure ɓarawon ne bayan ya amsa laifinsa a gaban kotu.
Rundunar ’yan sandan Abuja ce ta gurfanar Terkaa bayan ya saci wayar salula da Alqur’anai guda biyu a wani masallacin da ke barikin sojojin a unguwar Asokoro.
Mai gabatar da kara, Emeka Ezeganya ya ce, laifin da Terkaa ya aikata na keta haddi da kuma sata ya ci karo da sashe na 348 da kuma na 287 a kundin final kod.
- Akpabio Na Shan Caccaka Kan Batun Kisan Sojoji A Delta
- Abin Da Ake Yi A Goman Tsakiyar Ramadan A Addini Da Al’ada
Mista Ezeganya, ya ce wata mai suna Balikisu Isah da ke barikin sojin a Asokoro ce ta kai kara wurin ‘yan sandan yankin.
Bayan gudanar da bincike ne ‘yan sanda suka mika shi ga kotu domin a hukunta shi daidai da laifinsa.
Alƙalin ya bai wa Terkaa zaɓin biyan tara ta Naira Dubu Arba’in ko kuma zaman kaso na watanni 15, kamar yadda Kamfanin Dillacin Labaran Najeriya NAN ya bayyana.