Fursunoni a wannan Juma’ar sun gudanar da zanga-zanga a gidan gyaran halin Jos da ke Jihar Filato saboda yunƙurin mahukunta na rage musu kasafin abinci.
Aminiya ta ruwaito cewa, boren da fursunonin ke yi na zuwa ne bayan sun samu labarin cewa akwai tsare-tsaren da hukumar kula da gidajen yari ta yi na fara sassabe kasafi da kuma rage ingancin abincin da ake ba su.
- Tinubu ya bukaci sojoji su kawo karshen ‘yan bindiga a Arewa
- Likitoci 38 sun yi nasarar tiyatar raba tagwayen Najeriya
Bayanai sun ce dangane da wannan bayanan sirri da masu zaman waƙafin suka samu ne suka ɗaura ɗamarar ganin ba a yi musu sagegeduwa ba a fannin abincinsu.
Wasu daga cikin martanin da fursunonin suka aiwatar sun haɗa da bijere wa umarnin gandirebobi sabanin yadda suka saba yi musu ladabi a baya, da kuma ƙaurace wa yin karin kumallon safe da kafa dandazo a tsakar gidan zaman ɗan Kanden, lamarin da aka riƙa watsa musu barkonon tsohuwa domin kora su ɗakunansu.
Aminiya ta tuntubi Kwanturolan Gidan Yarin Jos, Raphael Ibinuhi, ya tabbatar da faruwar lamarin.
A cewarsa, “matsalar da muke fuskanta a yanzu ita ce farashin kayayyakin abincin sun yi tashin gwauron zabi a kasuwa.
“Sannan kuma jami’in da ke kwangilar abincin ya ce tsadar kayayyakin a kasuwa ce ta sanya dole za su rage kasafin abincin da ake raba wa fursunoni.
“Saboda haka wannan mataki ne ya fusata fursunonin suke bore.
“Sai dai kuma ina ganin wannan boren da fursunonin suka yi bai dace ba la’akari da cewa matsalar tsadar abinci da sauran kayayyaki ta gama-gari wadda kuma gwamnati tana ƙoƙarin ganin ta yi wa tufkar hanci.
“Saboda haka tunda wannan matsala ce ta gama-gari da ta shafi kasa baki ɗaya, duk wani mataki da gwamnati ke ɗauka domin magance ta sai an ji raɗaɗin ta a ko’ina hatta a gidajen gyaran hali.”