Wata Babbar Kotun Tarayya da ke zamanta a Jihar Legas, ta daure Idris Okuneye wanda aka fi sani da Bobrisky a gidan gyaran hali, ba tare da zaɓin tara ba.
Alƙalin kotun, Mai shari’a Abimbola Awogboro, ya yanke wa Bobrisky hukuncin ɗaurin wata shida a gidan gyaran hali.
- Kotu ta bayar da belin Emefiele kan miliyan 50
- HOTUNA: Yadda Sarkin Fulanin Legas Ya Yi Hawan Idin Karamar Sallah
Hukumar Yaƙi da Masu Yi Wa Tattalin Arziƙin Ƙasa Zagon Ƙasa (EFCC) ce, ta kamar Bobrisky tare da gurfanar da shi a gaban kotu kan zargin wulaƙanta takardun Naira
Bayan gurfanar da shi, Bobrisky ya amsa laifin da ake tuhumarsa da shi, inda ya nemi kotun ta yi masa afuwa.
Kafin samunsa da laifi, Bobrisky ya shaida wa kotu cewa ba shi da masaniya kan dokar hana wulaƙanta naira.
Alƙalin kotun, ya shaida masa cewa rashin sani ba hujja ba ne a doka.
Bobrisky ya kuma nemi alƙali da ya sake ba shi dama ta yin amfani da shafinsa na sada zumunta wajen ilmantar da mabiyansa game da illar yin liƙi da kuɗi.
“Ina da tarin mabiya fiye da miliyan biyar. Zan ɗora bidiyo a shafina kuma na faɗakar da mutane game da yin liƙi da kuɗi. Ba zan sake yi ba, na yi da na sanin abubuwan da na yi.”
Bobrisky dai na iya fuskantar hukuncin wata shida a gidan yari ko biyan tarar naira dubu 50 ko ma ya yi duka biyun.
Aminiya ta ruwaito cewa, a makon da ya gabata ne EFCC, ta kama Bobrisky saboda zarginsa da wulaƙanta takardun kuɗi na naira.
EFCC ta bayyana cewa ta gayyaci Bobrisky bayan ɓullar wani bidiyo da ke nuna yadda mai shekara 31 a duniyar ke yin liƙi da sabbin banduran takardun naira.
Hukumar ta ce bidiyon ya naɗo Bobrisky yana watsi da takardun kuɗin a bikin nuna wani fim mai suna Ajakaju wanda jarumar Nollywood, Eniola Ajao ta shirya da aka yi ranar 24 ga watan Maris a shagon Film One Circle Mall da ke Lekki a Jihar Legas.
Sanarwar ta ce a baya ma an samu Bobrisky da aikata laifin da ake zargi a wasu tarukan sharholiya, kamar yadda EFCC ta ce bincike ya nuna.
A cewar hukumar, Bobrisky ya amsa gayyatar da ta yi masa kuma da safiyar ranar Laraba ya bayyana a ofishinta na Legas domin amsa tambayoyi.