Wata Kotun Majistare da ke birnin Ibadan a Jihar Oyo, ta bayar da umarnin tsare wasu ‘yan’uwa juna biyu: Latunde Alayemi da Ayoola Alayemi a gidan gyaran hali kan zarginsu da kashe wani mutum mai shekara 49.
Alƙalin kotun, Misis Kausarat Ayofe, wadda ba ta amsa roƙon waɗanda ake ƙara ba ma bayar da belinsu.
- Mahaifiyar Rarara: Masu garkuwa na neman N1bn
- DAGA LARABA: Digiri Ko Sana’a —Wanne Ya Fi Muhimmanci?
Ta kuma umarci ’yan sanda da su mayar da takardun ƙarar ga daraktan shigar da ƙara na ƙasa (DPP), domin neman shawara sannan ta ɗage sauraron ƙarar zuwa ranar 2 ga watan Satumba.
Tun da farko, ɗan sanda mai shigar da ƙara, Insifekta Toyin Ibrahim, ya shaida wa kotun cewa waɗanda ake tuhumar a ranar 23 ga watan Yuni a unguwar Moniya da ke Ibadan, sun yi sanadin mutuwar wani David Olagoke, ta hanyar saran jikinsa.
Ya ce laifin ya saɓa da sashe na 516 da 324 na kundin laifukan Dokokin Jihar Oyo na 2000.