Wata babbar kotu a Jihar Kano ta bayar da umarnin dakatar da shugabannin rikon kungiyar Masu sayar da motoci ta Jihar Kano (MUDAKAS) sakamakon karar da Ambassada Muktari Gashash ya shigar gabanta, inda yake kalubalantar shugabancin nasu.
Shugabannin kungiyar da Ambassadan ya yi kara sun hada da Alhaji Sani dantata da Alhaji Ado Yakasai da Bawa Mohammed Habib da Alhaji Salisu dansalo da Alhaji Ado Gwarjo da danjuma Jigilawa da Alhaji Bala Mohammed Kabara da kuma Alhaji Shehu Aliko koki.
Umarnin kotun bai tsaya kawai ga dakatar da mutanen a ayyana kansu a matsayin shugabannin kungiyar da kuma matsayinsu na kwamitin amintattunta ba, har ila yau ta hana su taba ko sisi daga asusun kungiyar. Haka kuma an hana su karbar ko sisi daga hanun ’ya’yan kungiyar da sunan kudin rajista ko kuma na sabunta katin shaida.
Kotu ta dakatar da shugabannin kungiyar MUDAKAS
Wata babbar kotu a Jihar Kano ta bayar da umarnin dakatar da shugabannin rikon kungiyar Masu sayar da motoci ta Jihar Kano (MUDAKAS) sakamakon karar…