✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Zaben Edo: Kotu ta dakatar da Obaseki daga yin takara a PDP

Kotu ta hana Gwamnan Jihar Edo Godwin Obaseki shiga zaben fitar da dan takarar jam’iyyar PDP a zaben gwamnan jihar na a watan Satumba, kwana…

Kotu ta hana Gwamnan Jihar Edo Godwin Obaseki shiga zaben fitar da dan takarar jam’iyyar PDP a zaben gwamnan jihar na a watan Satumba, kwana biyu tak kafin zaben fid da gwani.

Babbar Kotun Tarayya da ke zamanta a Fatakwal, Jihar Ribas ta yanke hukuncin ne a safiyar Talata bayan karar da daya daga cikin ‘yan takara a zaben fitar da gwanin na ranar Alhamis, Omoregie Ogbeide-Ihama  ya shigar a gabanta.

Alkali E.A Obile, ya amince da bukatar mai karar na hana Obaseki shiga zaben fidda gwamnin kuma ta dage sauraren karar zuwa Laraba 24 ga watan Yuni, wato jajibirin zaben, domin ba wa bangaren da ake kara takardun sammacin da ake bukata.

A ranar Litinin ce Omoregie Ogbeide-Ihama ya lashi takobin kin janyewa daga neman tsayawa takarar sannan ya shigar da kara gaban Kotun.

Obaseki ya koma jam’iyyar PDP ne a ranar Juma’a domin neman takara, mako guda bayan jam’iyyarsa ta APC ta hana shi neman sake tsayawa takarar kujerarsa.

A ranar Juma’ar Kwamitin Gudanarwar Jam’iyyar ta Kasa ta sahale masa yin hakan duk da cewa bai cika tsawon lokacin da ya kamata ya kai a cikin jam’iyyar kafin ya iya yin takara ba. A ranar Asabar jam’iyyar ta tantance shi domin shiga zaben tsayar da dan takara.

Jam’iyyar PDP na ganin Obaseki zai kai ta ga nasara a zaben gwamnan, inda Kwamitin Amintattunta ya nuna amincewa da sassaucin da aka yi masa tare da kira da a yi zabe na gaskiya domin fitar da dan takarar da zai daga tutar jam’iyyar a zaben na ranar 25 ga watan Satumba.