Babbar Kotun Jihar Kano a ranar Alhamis ta dakatar da gwamnatin Jihar daga rusa gine-ginen da aka yi a jikin badalar (ganuwar) da ke kan titin BUK Road a birnin Kano.
Tuni dai gwamnatin, ta hannun Hukumar Tsara Birane ta Jihar (KNUPDA) ta shafa wa gine-ginen, wadanda suka hada da katafarun shaguna da gidajen mai, jan fenti, da nufin rushe su.
- Za a kashe wa sababbin ’yan majalisa biliyan 70 a matsayin kudaden ‘maraba’
- Majalisa ta sahale wa Tinubu ya kashe N500bn don rage radadin cire tallafin mai
Lamarin dai, a lokacin da KNUPDA ta shafa jan fentin ya janyo ce-ce-ku-ce a ciki da wajen Jihar, inda wasu ke cewa za a yi barnar dukiya.
Gwamnatin dai ta ce an yi gine-ginen ne a kan filayen badalar Kano, wacce ta ce gwamnatin tsohon Gwamna Abdullahi Umar Ganduje ta sayar da su ga mutane ba bisa ka’ida ba.
To sai dai bayan matakin na KNUPDA, mamallaka gine-ginen sun garzaya gaban babbar kotun inda suka nemi ta dakatar da gwamnatin daga aiwatar da kudurin nata.
Alkalin kotun, Mai Sharia’a Hafsat Yahaya, ta bayar da umarnin wanda ya dakatar da Gwamnan Jihar, Abba Kabir Yusuf da wasu mutum uku da ake karar daga rusau din.
Ragowar wadanda aka yi karar dai sun hada da Babban Lauyan Gwamnatin Jihar da Hukumar da ke Lura da Harkar Filaye ta Jihar da kuma hukumar KNUPDA.
Daga nan ne kuma kotun ta dage ci gaba da sauraron karar har zuwa ranar 26 ga watan Oktoba mai zuwa.