✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kotu ta ci maigadi tarar N530,000 kan satar na’urar dumama ruwa

Kotu ta umarci maigadib ya biyan diyyar N530,000 ga ubangidan nasa

Wata kotu a Abuja ta yanke wa wani maigadi hukuncin daurin wata uku a kurkuku tare da biyan diyyar N530,000 kan sace wa ubangidansa na’urar dumama ruwa.

Kotun da ke zamana yankin Dei-Dei ta kuma umarci maigadin ya biyan diyyar N530,000 ne ga ubangidan nasa.

Da yake yanke hukucin za aman koun na ranar Laraba, alkalin kotun, Saminu Suleiman ya kuma bai wa maigadin zabin biyan tarar N30,000 ko zaman gidan yari.

Tun farko, lauyan mai gabatar da kara, Mista Olanipekun Babajide, ya shaida wa kotun cewa har da katifa maigadin ya hada ya sace.

Ya kara da cewa wanda ake zargin ya hada kayan da a sace sannan ya sayar a kan N19,000 kuma ya amsa laifinsa a yayin binciken ’yan sanda.